Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Jirgin Ruwan Dakon Jiragen Yakin China Ya Nufi kudancin Tsibirin Taiwan


China Taiwan
China Taiwan

Taiwan ta bada rahoton hango wani jirgin ruwan dakon jiragen yakin China da ya nufi kudancin tsibirin a ranar Lahadi.

A wani labarin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa ya ce, Taiwan ta ruwaito hango wani jirgin ruwan dakon jiragen yakin China da ya nufi kudancin tsibirin a ranar Lahadi, yayin da sojojin China suka kafa wani faifayin bidiyo suna cewa “munyi shirin yaki”, a sa’adda ake zaman fargaba a Tapei kan yiwuwar China ta sake takalo wani sabon salon yaki.

China, ta dauki yankin Taipei dake karkashin tsarin demokradiyya a matsayin yankin ta ne, bata son shugaban ta Lai Ching-te wanda ta dauke shi a matsayin “dan aware” sannan sojojin China suke gudanar da atisayen soji a daura da tsibirin.

A jawabin da ya gabatar na musamman a ranar bukin kasar a makon jiya, Lai ya ce jamhuriyar China bata da wani ‘yancin wakiltar Taiwan, amma a shirye tsibirin take tayi aiki tare da Beijing don shawo kan matsalolin sauyin yanayi, a lokaci guda ya bayyana iko da shirin yin sulhu da fushi akan China.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG