Hezbollah ta ce tayi ruwan makama mizal da suka auna wani sansanim sojin Isra'ila a ranar asabar, a dai dai sa'adda da dakarun Isra'la suke ci gaba da fafatawa da mayaka a Lebanon da Gaza, a ranar Yom Kippur, rana mai daraja a adinin yahudu.
Mutane sun dauke kafa a biranen dake kewaye da Isra’ila yayin da kasuwani suka kasance a rufe, an kuma dakatar da zurga zurgar jiragen sama da motocin sufurin kasuwa yayin da yahudawa suka dukufa azumi da addu’o’I a ranar da ake ayyana shi da ranar neman rahama.
Sai dai, kasancewar kasar ta Isra'ila tana yaki da Hezbollah da Hamas, dakarun na Isra’ila sun ci gaba da fafatawa a yankin arewaci da kudanci a daidai lokacin da kasar take fuskantar suka akan raunata ma’aiktan Majalisar Dinkin Duniya masusu aikin tabbatar da zaman lafiya a Lebanon.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ta bada rahoton cewa,
Mayakan Hezbollah, sun yi ni niyyar auna inda ake sarrafa abubuwan fashsewa ne da suka kai harin makaman na mizal, abin da kungiyar ta fada cikin wata sanarwa kenan.
Dandalin Mu Tattauna