Shugaban Amurka Joe Biden ya yi magana da Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a ranar Laraba, inda ya sake tabbatar da cikakken goyon bayansa ga Isra’ila.
Tattaunawar shugabannin biyu ta wayar tarho na zuwa ne yayin da Isra’ilan ke ci gaba da kai hare-haren soji kan mayaka a Gaza da Lebanon tana kuma duba zabin da take da shi wajen mayar da martani hare-haren makamai masu linzami da Iran ta harba mata.
Wannan kira na waya shi ne na farko tun bayan wanda suka yi a ranar 21 ga Agusta.
Fadar White House ta ce Mataimakiyar Shugaban kasa Kamala Harris ta shiga cikin kiran.
Kakaki a Fadar Gwamnatin Amurka ta White House Karine Jean-Pierre ta shaida wa manema labarai cewa kiran "ya kasance kai-tsaye kuma mai ma'ana" kuma ya dauki kusan rabin awa.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Fadar White House ta ce shugabannin sun tattauna "bukatar gaggawa na dawo da diflomasiyya domin ganin an saki mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su" a Gaza tare da magance matsalolin da al’umar Gaza ta shiga.
Netanyahu yana ta nazarin zabin da yake da shi domin maida martani ga Tehran bayan da ta harba kusan makamai masu linzami 200 kan Isra’ila a ranar 1 ga Oktoba.
Harin shi na a matsayin babban matakin da ke nuna tsanantar rikicin da aka kwashe shekara guda ana yi tsakanin Isra’ila da kawayen Iran da ke yankin Gabas ta Tsakiya.
Dandalin Mu Tattauna