Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra'ila Sun Gargadi Al'ummomin Kusa Da Iyakar Lebanon Su Kaurace


Israel-Lebanon
Israel-Lebanon

A yau Talata, rundunar sojin Isra'ila ta gargadi al'ummomin dake zaune a yankunan kan iyakar Lebanon dasu kaurace daga kusan garuruwa 24 bayan da ta kaddamar da samamen da ta kira da kwarya-kwaryan kutse ta kasa akan mayakan kungiyar Hezbollah

Hezbollahi ta musanta cewar dakarun Isra'ila sun shiga ta kasa sai dai tace a shirye take ta tunkaresu.

Israel-Lebanon
Israel-Lebanon

Sojin Isra'ila sun shawarci jama'a su kaurace daga yankin arewacin kogin Alwali, mai nisan kusan kilomita 60 daga kan iyakar kuma ya dan fi tazara daga kogin Litani, wanda ya kasance kuryar arewacin yankin da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana a matsayin iyakar da ta raba tungar dakarun Isra'ila da mayakan Hezbollah bayan yakin da suka gwabza a 2006.

"Wajibi ne ku gaggauta matsawa zuwa yankin areawacin kogin Alwali domin tsira da rayukanku tare da barin gidajenku nan take," a cewar sanarwar da kakakin sashen Larabci na rundunar sojin Isra'ila, Avichay Adraee ya wallafa a shafinsa na X.

Kauyukan Adeisseh da Kfar Kila kusa da iyakar Isra'ila Oktoba 01, 2024.
Kauyukan Adeisseh da Kfar Kila kusa da iyakar Isra'ila Oktoba 01, 2024.

Yankin kan iyakar ya kasance babu mutane a cikinsa a shekara guda data wuce sakamakon musayar wutar da bangarorin 2 suka jima suna yi da juna. Sai dai fadin yankin da Isra'ilar ta umarci al'umma su tashi daga cikinsu ya janyo ayar tambaya akan irin nisan yankunan da take nufin tura dakarunta a kasar Lebanon a daidai lokacin da take zafafa kai hare-hare akan kungiyar Hezbollahi.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG