Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Yi Hasashen Hatsarin Fadadar Yaki Bayan Kashe Shugaban Hezbollah


Lebanon-Russia
Lebanon-Russia

A yau Litinin, fadar Kremlin ta yi Allah-wadai da kisan Shugaban Hizbullahi Hassan Nasrallah da hare-haren Isra’ila ta sama su ka yi a makon da ya gabata sannan tace tana da hasashe mai karfi dake nuna yiyuwar fadadar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.

APTOPIX Pakistan-Israel-Lebanon
APTOPIX Pakistan-Israel-Lebanon

Kakakin fadar Kremlin Dimitry Peskov ya shaidawa manema labarai cewar, “mu a matsayinmu na Rasha muna allawadai da wannan mataki, kuma muna da yakinin cewar hakan zai sake ta’azzara al’amura a yankin.”

Ya kara da bayyana damuwar mahukuntan birnin Moscow inda yace, “babban al’amarin shine kai hare-haren bam a kan unguwannin zaman jama’a zai haifar da mummunar asarar rayuka, wacce za ta janyo bala’in neman agaji kamar wanda muke gani a zirrin Gaza.”

Gaza
Gaza

Zafafa kai hare-haren da Isra’ila ke yi a kan Hezbollah ya kara damuwar da al’ummar duniya ke da ita game da hatsarin fadadar yakin a yankin Gabas ta Tsakiya wanda ka iya janyo kasar Iran, dake marawa kungiyoyin Hezbollah da Hamas baya.

Sergei Lavrov
Sergei Lavrov

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya bayyana kisan Nasrallah da aka yi a karshen mako a matsayin wanda ke da alaka da siyasa, sannan sanarwar da ma’aikatar wajen Rashan ta fitar ta bukaci Isra’ila da ta gaggauta dakatar da hare-haren da take kaiwa a Lebanon.

-AP/Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG