Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda NNPC Ya Yi Fatali Da Tayin Dangote Na $750m Domin Gudanar Da Matatun Man Najeriya - Obasanjo


Olusegun Obasanjo
Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya ce NNPC ya san cewa ba shi da karfin da zai iya gudanar da matatun man Najeriya amma duk da hakan ya yi fatali da tayin na Dangote.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bada labarin yadda kamfanin man fetur din Najeriya (NNPC) ya yi fatali da tayin dala miliyan 750 da hamshakin dan kasuwar nan Aliko Dangote ya yi a 2007 domin gudanar da matatun man Fatakwal da Kaduna.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin wata kebabbiyar hira da tashar talabijin ta Channels.

Ya kara da cewa NNPC, da yanzu aka sauyawa fasali zuwa NNPCL, ya san cewa ba shi da karfin da zai iya gudanar da matatun man Najeriya amma duk da hakan yayi fatali da tayin na dangote.

A cewar Obasanjo, "Aliko ya hado tawaga sannan suka biya dala milyan 750 domin shiga kawance tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa (PPP) da zai gudanar da matatun man. shugaban daya gaje ni ya mayar musu da kudinsu don haka naje na same shi na shaida masa abinda ya faru. Ya shaida mini cewar nnpc yace yana bukatar matatun kuma zai iya gudanar dasu. nan take nace masa kasan ba zasu iya gudanar dasu ba."

Obasanjo ya kasance zabebban shugaban najeriya tsakanin watan Mayun 1999 da Mayun 2007. kuma ya kasance shugaban mulkin sojan kasar tsakanin watan Febrairun 1976 da Oktoban 1979.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG