Bayanai sun nuna cewa gwamnan na jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya ba da umurnin ga hukumar kula da malamai na jihar ta dauki malaman sakandare guda dubu daya, daga bisani gwamnatin ta rika samun korafe-korafe daga jama'a cewa ta ki biyan malaman da ta dauka aiki.
Lamari kenan da yasa gwamnatin ta fara kaddamar da bincike, inda ta gano cewa hukumar ta dauki karin malamai fiye da dubu daya wanda gwamnati bata yi tanadi domin biyansu albashi ba.
Kwamishinan Ilimi na jihar Nasarawa, Honarabul John Mamman yace gwamnatin ta dakatar da shugaban hukumar da sauran ma'aikatan hukumar ta kuma nada kwamiti don gudanar da bincike.
Wani da ya bukaci a sakaya sunansa, yace ya sayar da gonar gado, ya sayi aikin kan kudi naira dubu dari takwas da hamsin, an bashi takardar daukan aiki har yayi aiki na watanni hudu, sai aka ce yana cikin wadanda aka dauka ba bisa ka'ida ba.
Kokarin jin ta bakin shugaban hukumar kula da malaman na jihar Nasarawa, Abubakar Muhammad Gada, ya ci tura, duk da kira da sako da wakiliyar Muryar Amurka ta aike masa.
Shugaban kungiyar matasan jihar Nasarawa, Ja'afar Loko ya ce suna goyon bayan gwamnati ta gudanar da bincike kan lamarin.
Shima wani dan gwagwarmaya a jihar ta Nasarawa, Bukhari Abdullahi Nata'ala ya ce batun saye da sayar da ayyuka da jami'an gwamnati ke yi ya zame matsala.
Yanzu dai ana jiran sakamakon binciken kwamitin da kuma matakin da gwamnatin jihar Nasarawa za ta dauka.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:
Dandalin Mu Tattauna