Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Bukaci A Kawo Karshen Hare-Haren Isra'ila A Gaza


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

A jawabinsa ga taron kolin kasashen Larabawa da Musulmi wanda aka shirya da nufin magance halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, Tinubu ya bayyana matukar damuwa game da yanayin ayyukan agaji da Gaza ke ciki.

A yau Litinin a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya bukaci a kawo karshen hare-haren Isra'ila a Gaza, inda ya yi gargadin cewa rikicin Falasdinu ya jima yana gudana, tare da haifar da dimbin wahalhalu "

A jawabinsa ga taron kolin kasashen Larabawa da Musulmi wanda aka shirya da nufin magance halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, Tinubu ya bayyana matukar damuwa game da yanayin ayyukan agaji da Gaza ke ciki.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwa da mashawarcin shugaban Najeriya na musamman a kan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Litinin.

Ya kara da cewa, taron na yini guda dori ne a kan irinsa daya gudana a birnin Riyadh a bara wanda ya samu halarcin shugabannin kungiyar kasashen musulmin duniya (OIC) da na kungiyar kasashen Larabawa.

"Rikicin Falasdinu ya jima yana gudana, ya haifar da dimbin wahalhalu ga rayuka da dama.

“A matsayinmu na wakilan kasashe dake martaba adalci da mutunci tare da mutunta ran dan adam, akwai hakkin daya rataya a wuyan dukkaninmu na gaggauta kawo karshen wannan rikicin.

"Ba zai wadatar ba mu ci gaba yin tir da allawadai ba tare da daukar mataki ba. Wajibi ne duniya ta dauki matakin kawo karshen hare-haren Isra'ila a Gaza, abin da ya jima yana faruwa” in ji shugaban Najeriyar.

Da yake jaddada bukatar Najeriya ta gaggauta tsagaita wuta a Gaza, Tinubu ya tabbatar da goyon bayan kasarsa ga warware rikicin ta hanyar samar da kasashe 2, inda dukkanin Isra'ila da Falasdinu zasu wanzu tare cikin tsaro da mutuntawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG