Wata arangama tsakanin 'yan bindiga da 'yan banga a garin Goronyo na jihar Sakkwato ta yi sanadiyyar kashe 'yan banga hudu, da 'yan bindiga da ba'a san adadinsu ba, baya ga wani hari a yankin Wurno da ya yi sanadin mutuwar mutum hudu.
'Yan Najeriya sama da miliyan daya ne za su rasa ayyukanşu a karkashin shirin tallafin yaye talauci na N-Power na Gwamnatin tarayyya, biyo bayan dakatar da shirin da Gwamnati ta yi na tsawon lokaci.
Bankin Duniya ya wallafa wani rahoto da ke cewa tun daga tsakiyar watan Yuni na shekarar 2023 darajar Naira ta ragu da kashi 40 cikin 100. Wannan ya nuna cewa naira ta zama kudi mafi lalacewa a cikin kudaden da ake kasuwanci da su a kasashen Afirka. Masana sun tofa albarkacin bakinsu.
Juye-juyen mulki da kara nuna kyama ga Faransa a Yammaci da Tsakiyar Afirka na da muhimman darussa na siyasa da na soja ga gwamnatocin Afirka da abokansu na duniya, kamar yadda manazarta suka shaida wa Muryar Amurka.
Fadar Shugaban Najeriya ta musanta dukkan zarge-zargen da Atiku da lauyansa suka yi kan takardun karatun Tinubu.
Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna da ke zaman ta a jihar Kebbi ta yi watsi da karar da jam'iyar PDP da ‘dan takarar ta Manjo Janar Aminu Bande mai ritaya suka shigar kan zaben gwaman Nasir Idris Kauran Gwandu na Jam'iyar APC da mataimakinsa Umar Abubakar Tafidan Argungu.
Har yanzu 'yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare ga al'ummomi a Arewacin Najeriya, kamar yadda yake gudana a jihar Sakkwato da ke Arewa maso yammacin kasar.
Ko da yake, ba a fayyace abin zai yi magana a kai ba, amma wasu na ganin taron manema labaran bai rasa nasaba da batun takardun karatun Bola Ahmed Tinubu da Jami'ar Chicago da ke Amurka ta fitar.
Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da sace dalibai mata biyar na jami'ar tarayya da ke Dutsin-Ma a jihar Katsina ranar Laraba a gidan da suke zama.
Cikin dalilan akwai batun ba iyalai miliyan 15 Naira dubu 25,000 daga watan nan na Oktoba zuwa watan Disamba na 2023, amma kungiyoyin kwadagon sun ce suna jira su ga an cika alkawari nan da wata daya in ba haka ba za su ci gaba da yajin aiki.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.