Jiragen yakin Najeriya sun sami nasarar auna mabuyar ‘yan ta'addar Boko Haram a zirin tafkin Chadi, yankunan Tumbun Fulani da Tumbun Shitu inda ake ganin na zama barazana ga cibiyoyin soji da ma al'ummar yankunan.
Gwamnatin Tarayya da Kungiyoyin Kwadago sun tashi daga taron da suka yi a ranar Lahadi inda suka cimma matsaya kan cewa dukkan ma'aikata za su ci gajiyar karin albashi na wucin gadi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a jawabin da ya yi wa kasa, yayin bikin tunawa da ranar samun 'yancin kai.
Asusun koyar da harshen Larabci na Najeriya ya yi alwashin amfani da gwanancewa a harshen wajen yaki da akidar ta’addanci a Najeriya da kasashen yankin Sahel.
Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani game da hukuncin babbar kotun tarayya da ya umarci gwamnatin ta biya diyyar naira biliyan 30 ga ‘yan kasuwar da ta rusa wa shaguna da gine gine a gefen babban Masallacin Idi na Kano kimanin watanni uku da su ka gabata.
Naira Marley da Sam Larry sun sha musanta hannu a mutuwar MohBad, wanda ya rasu cikin wani yanayi mai sarkakiya.
Tun bayan da aka sa samu bullar cutar Mashako a watan Disambar 2022 a Najeriya, kasar ke bin hanyoyin dakile yaduwar ta, sai dai yanzu abin ya fara zama abin damuwa ga hukumomin lafiya.
Daya daga cikin manyan kungiyoyin man fetur da iskar gas a Najeriya za ta shiga yajin aikin da za a fara daga ranar 3 ga watan Oktoba a fadin kasar domin nuna adawa da manufofin gwamnati da ke janyo wa 'yan Najeriya kuncin tabarbarewar tattalin arziki, in ji shugabannin kungiyoyin a ranar Alhamis.
Tsarin inshorar da a ke kira Takaful ya kara samun tagomashin raba rarar kudi ga wadanda suka shiga tsarin da samun miliyoyin Naira.
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya amince da sallamar shugabannin ma’aikatu da kamfanonin gwamnati 21 da ke karkashin birnin na Abuja.
Jama’a da dama na ta dora alhakin mutuwar Mohbad akan Naira Marley wanda shi ne tsohon maigidansa da ya fara daukansa a aiki a kamfaninsa na Marlians. Naira Marley ya musanta zargin.
Kungiyoyin kwadago biyu mafi girma a Najeriya na shirin fara yajin aikin sai baba-ta-gani a mako mai zuwa domin nuna adawa da matsalar tsadar rayuwa bayan da gwamnati ta yi watsi da tallafin man fetur mai tsada.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.