Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsadar Gas Ta Sa Mutane Sun Fara Koma wa Amfani Da Makamashin Itace A Najeriya


Iacen girki
Iacen girki

‘Ƴan Najeriya na nuna damuwarsu game hauhawar farashin makamamashin iskar gas, wanda yanzu haka farashin yakai naira 12,500 ga kowanne kilo 12 da rabi, wanda tsadar tasa magidanta komawa gidan jiya, wajen amfani da itace ko kuma gawayi domin yin girki da sauran sana'o'i.

Baya ga halin ƙunci na tsadar kayayyakin rayuwar yau da kullum da ƴan ƙasar ke fama dashi, wani sabon ƙalubale da ya kunno kai a ƴan kwanakin nan, shine tsadar iskar Gas.

Tukunyar Iskar Gas
Tukunyar Iskar Gas

A watanni biyu baya dai farashin iskar Gas a Najeriya, Naira 560 ga kowanne ma'aunin kilo, sai dai yanzu farashin ya haura Naira 950, wanda hakan ya jawo al'ummar ƙasar komawa gidan jiya, wato amfani da makamashin itace wajen girke-girke.

Yakubu Ali Bulkadimka, me kula ne na musamman a ƙungiyar dillalan Man-Fetur ta IPMAN ya ce "tsadar da dalar Amurka tayi, da kuma sauran tsarabai ne ke haddasa hauhawar farashin, wanda hakan ka iya tilasta su rufe wuraren da suke sayar da iskar Gas ɗin".

Gali Shitu mai sana'r sayar da Indomi ne, ya shaidawa Muryar Amurka cewa su yanzu sun haƙura da amfani da iskar Gas wajen sana'arsu ta sayar da Indomi, sun koma amfani da makamashin gawayi.

Girkin itace
Girkin itace

Yakubu Garba na ɗaya daga cikin ƴan Najeriya da sukayi bankwana wajen amfani da iskar Gas a gidajensu bisa tsadar da tayi, suka koma amfani da makamashin itace domin amfanin yau da kullum a gidajen su.

A hirarsa da Muryar Amurka, Dakta Mustapha Mala, masanin kan lamuran da suka shafi muhalli kuma Malami a Jami'ar Maiduguri, ya ce "sare itatuwa da mutane keyi yanzu bisa tsadar iskar gas da kalanzir, babban barazana ne ga muhalli, domin hakan zai haifar da yawaitar samun guguwa da kuma ɗumamar yanayi"

Farfesa Binbol Nankap, Shugaban Tsangayar ilimin kimiyyar Muhalli ne dake Jami'ar Jos, ya ce " baya ga zaizayar hamada, sare bishiyoyi na daga cikin abinda ke jawo ƙarancin ruwan sama a yankin Arewacin ƙasar," ya kuma shawarci al'umma da su dasa bishiyoyi domin kula da muhalli, maimakon sare su da akeyi.

Muryar Amurka ta yi ƙoƙarin tuntuɓar hukumar dake kula da sha'anin farashin albarkatun man-fetur NMDPRA, sai dai basu amsa ƙira da kuma saƙon da aka aika musu ba, har izuwa haɗa wannan rahoto.

Saurari rahoton Ruƙaiya Basha:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG