Kungiyar, mai suna WANDA Organization mai rajin bunkasa ilimin 'ya 'ya mata akan nazarin kimiyyar sarrafa abinci da samar da shi, ta dauki nauyin karatun dalibai 30 dake karatu a Jami’ar Bayero Kano wadanda ke nazari a fannin kimiyyar sarrafa abinci da dangoginsa.
Kotun daukaka kara dake zama a Abuja, ta soke zaben Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Simon Mwadkon dake wakiltar jihar Filato ta Arewa a karkashin jami'iyyar PDP.
Rahotanni sun ce 'yan fashin sun kwashe sama da sa'a guda suna sata a bankuna kafin daga bisani su arce.
Allah ya yi wa Jakadan Najeriya a kasar Morocco, Alhaji Mansur Nuhu Bamalli rasuwa yana da shekara 42.
Lauyoyi da masu sharhi kan lamuran siyasa na mara baya ga dawo da shari'un karar zaben 2023 ga kotun daukaka kara ta Abuja da Legas.
A Najeriya yayin da mahukunta ke kokarin lalubo mafita ga matsalar tsaro, su kuwa 'yan bindiga sai ci gaba suke yi da addabar jama'a ta hanyar kisa da yin garkuwa da su.
Atiku da sauran 'yan takarar na kalubalantar takardun karatun da Tinubu ya yi a Jami'ar Chicago a Amurka wadanda suke ikirarin na boge ne, zargin da fadar shugaban kasa ta musanta.
Matsalar faduwar darajar kudin naira abu ne da ya kara ta’azzara musamman a makonnin bayan-bayan nan inda ake sayen dala daya a kan naira 995 zuwa dubu 1 da 100 kasancewar karancin dala a cikin Najeriya.
Tun a farkon shekara ta 2022 ne gwamnatin Najeriya ta amince tare da ba da kwangilar gina layin dogo daga Dutse zuwa Kano da kuma Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar, da nufin habaka harkokin sufuri da na hada-hadar kasuwanci a tsakanin Najeriya da Nijar.
Alamu na nuna cewa watakila za a samu saukin matsalar rashin tsaro dake addabar wasu yankuna na Arewacin Najeriya saboda wasu gwamnoni sun fara nuna da gaske su ke yi.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nada Dakta Musa Adamu Aliyu a matsayin sabon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC yayin da ya kuma nada Mista Clifford Okwudiri a matsayin sakataren hukumar.
Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kashe diyar dan majalisa jihar Borno da ke wakiltar mazabar Ngala, Bukar Abacha a gidanta da ke birnin Maiduguri a yammacin ranar Talata.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.