A cikin wata sanarwa da ya fidda, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ASP Sadiq Aliyu Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Sadiq ya kuma ce an kama wani mutum da ake zargi da ba ‘yan bindiga bayanan sirri kana an kama wasu da dama da ake zagin suna da hannu wajen sata da yin garkuwa da daliban da akasarinsu mata ne. A halin yanzu dai an kaddamar da bincike don gano inda daliban suke da kuma ceto su a cewarsa.
Da misalin karfe biyu na safiyar Laraba ne dai wasu ‘yan bindiga suka kai samame a wani gida da daliban jami’ar tarraya ke haya a garin Dutin-Ma da ke jihar Katsina.
Jami’in watsa labaran jami’ar Malam Habibu ya tabbar da sace daliban, amma ya ce ba a cikin makaranta suke ba. Ya kara da cewa hukumar makarantar da jami’an tsaro suna kokarin ganin an kubuto da daliban.
Wannan dai na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan da ‘yan bindiga suka sace daliban jami’ar tarayya da ke jihar Zamfara da ba'a tabbatar da adadinsu ba sannan a ‘yan kwanakin da suka gabata wasu ‘yan bindiga suka kutsa jami’ar Usman Dan Fodio da ke jihar Sokoto suka sace kayyan abinci.
Saurari cikakken rahoton Sani Shu’aibu Malumfashi:
Dandalin Mu Tattauna