Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da sace dalibai mata biyar na jami'ar tarayya da ke Dutsin-Ma a jihar Katsina ranar Laraba a gidan da suke zama.
Cikin dalilan akwai batun ba iyalai miliyan 15 Naira dubu 25,000 daga watan nan na Oktoba zuwa watan Disamba na 2023, amma kungiyoyin kwadagon sun ce suna jira su ga an cika alkawari nan da wata daya in ba haka ba za su ci gaba da yajin aiki.
Majalisar dattawa ta yi wa dokar ta na gudanarwa gyaran fuska, inda aka hana sanatocin farko yin takarar kujeran Shugaban Majalisar dattawa da na mataimakinsa.
'Yan sandan Sun tsare Azeez Fashola ne wanda aka fi sani da Naira Marley bisa tuhumar da ake masa da hannu a mutuwar Mohbad wani mawaki da yake karkashin wanda ake zargin kafin mutuwarshi.
Kasa da sa’o’i 24 da cimma sabuwar yarjejeniyar janye yajin aiki da kungiyar kwadago ta Najeriya ta tsara farawa a yau 3 ga watan Oktoban shekarar 2023, kungiyar ta yi karin haske a kan yadda yarjejeniyar yanzu ta banbanta da wadanda kungiyar ta yi a baya wanda aka saba yi da baki ba a kan takarda ba.
Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da kokawa dangane da tsadar albarkatun mai biyo bayan cire tallafin gwamnati tun kimanin watanni biyar da suka shude, masu gidajen man a yankin arewacin kasar sunce harkokinsu na fuskantar barazanar durkushewa, amma masana tattalin arziki sun ce akwai mafita.
Hukumar Ƴaki da Cin-Hanci da Rashawa ta EFCC ta samu damar tasa ƙeyar tsohuwar Ministar Albarkatun Man-Fetur Diezani Aliason Madueke zuwa gida Najeriya domin a gurfanar da ita a gaban kotu bisa zarginta da ake yi na halasta kuɗaɗen haram, a lokacin da take minista.
Mako guda bayan da 'yan bindinga suka sace daliban jami'ar gwamanatin tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, a cikin daren ranar Litinin wasu 'yan bindiga sun kutsa jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto suna harbe-harbe, inda suka yi awon gaba da kayan abinci da wasu kayayyakin amfani.
Wata fashewa da gobara a wata haramtacciyar matatar mai a yankin Naija Delta a Najeriya ta kashe mutane akalla 15, ciki har da wata mai juna biyu, kamar yadda mazauna yankin da kuma wata kungiyar rajin kare muhalli a kasar suka bayyana ranar Talata.
Bayanai na nuni da cewa ma'aikatan ceto na can suna kokarin neman gawarwakin wadanda suka nutse a ruwan don a yi musu jana'iza.
Da yake sanar da sakamakon taron ga manema labarai, Ministan Kwadago da Aiki, Simon Lalong ya ce, “Kungiyoyin NLC da TUC sun amince da dakatar da yajin aikin na tsawon kwanaki 30 da suka shirya yi a fadin kasar. ”
Shugaban Majalisar sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya aike wa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu sakon taya murnar zagayowar ranar cika shekaru 63 da samun ‘yancin kan Najeriya.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.