Karamar ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da wasu manyan jami’an gwamnatin Najeriya ne za su marawa Tinubu baya a tafiyar.
Shugaban hukumar gudanarwa da kasafi na Amurka, Shalanda D. Young ce za ta jagoranci tawagar.
Matakin ya samu karbuwa daga jamma'ar kasa r ta Ghana da masu sharhi da dama, kasancewar ana sa kyautata zaton matakin zai bunkasa harkokin kasuwanci, yawon bude ido, da musayar al'adu a fadin nahiyar Afirka.
Muhamed da kungiyar sa kan al’ummar ta Kel Ansar sun ce dakarun Mali da mayakan Rasha na Wagner ne suka kai harin.
A farkon watan Disamban 2024 ne wasu mutane dauke da bindigogi suka kutsa gidan Tchmgari, suka kuma yi awon gaba da shi jim kadan bayan dawowarsa daga tafiya.
Ghana na baiwa al'ummomin kasashen Afirka 26 damar shiga kasarta kyauta tare da baiwa 'ya'yan wasu kasashe 25 izinin shiga kasar bayan da suka isa can, inda 'ya'yan kasashe 2 ne kacal ke bukatar neman biza kafin su shiga
Gwamnatin mulkin sojan jamhuriyar Nijar ta ayyana tsarin kasafin kudaden shekarar 2025 wanda ya haura billion 3033 na kudaden CFA a yayin da illolin yakin Ukraine da na annobar COVID-19 ke ci gaba da shafar tafiyar tattalin arzikin duniya
Kasar Cote d’ivoire ta bayyana shirin ficewar dakarun Faransa daga kasar kafin karshen watan Janairun 2025 da muke ciki.
Tun saura kiris a shiga sabuwar shekara ta 2025 a Jamhuriyar Nijer ‘yan kasar ke bayyana fatan su game da kasar da ma mulkin sojan kasar a sabuwar shekara, ta la'akari da rayuwa mai tsada da suke fuskanta, da ma, yake yake da yan ta'adda da suka zagaye kasar.
Ministan harkokin wajen Bénin ya gayyaci mukaddashiyar jakadan Nijar a Cotonou domin bayyana bacin ran gwamnatin kasarsa dangane da zargin da shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya yi na cewa mahukuntan Benin na da hannu a abin da ya kira yunkurin haddasa hargitsi a Nijar
Domin Kari
No media source currently available