Ofishin jakadancin Amurka a Jamhuriyar Benin ya ba da sanarwar faduwar wani jirgi farar hula mai saukar ungulu, wanda rundunar sojan Amurka a nahiyar Afirka ta AFRICOM ke amfani da shi, domin ayyukan hadin gwiwa da dakarun kasar ta Benin a fannin kiwon lafiya.
A dajin Park W musamman wajen kan iyakokin kasashen Nijar, Benin da Burkina Faso ne ‘yan ta'adda suka afkawa daya daga cikin sansanonin soja mafi kunshe da kayan yaki na zamani na kasar Benin, inda suka hallaka sojoji da dama suka kuma arce da kayan aikinsu.
Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta bayyana shirin gudanar da bincike a matatar hadin gwiwar kasar da China wato SORAZ domin tantance abubuwan da suka wakana shekaru sama da 10 bayan kaddamar da ayyukanta
China na ci gaba da kokarin abota da kasashen Afurka saboda arzikin ma'adinai da nahiyar ke da shi.
Chadi da Senegal sun maida martani da kakausan murya bayan da Shugaba Macron ya bayyana cewa Faransa ce ta yi niyar kwashe sojojinta daga Afirka sabanin yadda ake ta shailar cewa korarsu aka yi daga nahiyar
Haka kuma, an rantsar da mataimakiyar shugaban kasa, Farfesa Jane Opoku-Agyemang, mace ta farko da ta taba rike wannan mukami a Ghana.
Farfesa Naana Jane Opoku-Agyemang ta zama mace ta farko da babbar jam’iyyar siyasa NDC ta Ghana ta zaba don tsayawa takarar mataimakiyar shugaban kasa.
Karamar ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, da wasu manyan jami’an gwamnatin Najeriya ne za su marawa Tinubu baya a tafiyar.
Shugaban hukumar gudanarwa da kasafi na Amurka, Shalanda D. Young ce za ta jagoranci tawagar.
Matakin ya samu karbuwa daga jamma'ar kasa r ta Ghana da masu sharhi da dama, kasancewar ana sa kyautata zaton matakin zai bunkasa harkokin kasuwanci, yawon bude ido, da musayar al'adu a fadin nahiyar Afirka.
Domin Kari
No media source currently available