Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Soke Visa Ga Duk 'Yan Afirka Masu Sha'awar Shiga Kasar


Daga hagu: Shugaba Akufo-Ado da Shugaba Ruto
Daga hagu: Shugaba Akufo-Ado da Shugaba Ruto

Matakin ya samu karbuwa daga jamma'ar kasa r ta Ghana da masu sharhi da dama, kasancewar ana sa kyautata zaton matakin zai bunkasa harkokin kasuwanci, yawon bude ido, da musayar al'adu a fadin nahiyar Afirka.

Shugaban kasar Ghana mai barin gado, Nana Akufo-Addo ya cika alkawarin da ya dauka na aiwatar da tsarin shiga Ghana ba da biza ba, ga duk 'yan Afirka masu fasfo, da nufin habbaka shige da fice da harkokin kasuwanci tsakanin kasashe a nahiyar. Shugaban ya jaddada hakan cikin jawabin sa na karshe ga majalisar dokokin Ghana, a kan halin da kasar take ciki.

Tuni bayanan shugaban ya ja hankalin masu sharhi da ‘yan kasa wadanda suka fara tofa albarkacin bakinsu.

Tun a watan Disamba na 2024 ne shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya sanar da shirin, amma a jawabin sa kan halin da kasar ke ciki na karshe, ya ce dokar ta fara aiki tun daga farkon wannan shekarar ta 2025.

Ya ce "Ina alfahari da amincewa duk 'yan Afirka damar shigowa Ghana ba tare da biza ba, wanda tuni dokar ta fara aiki daga ranar daya ga watan Janairun wannan shekarar. Wannan shi ne mataki na gaba mai ma'ana a bangaren ciniki ba shinge a nahiyar Afirka. Duk waɗannan abubuwan suna da mahimmanci ga tabbatar dakudurin Tarayyar Afirka.

Wakilin Muryar Amurka a birnin Accra Idris Abdallah Bako, ya ruwaito cewa masanin huldar kasa da kasa da al'amuran tsaro, Irbard Ibrahim yace, wannan mataki yayi kyau kana ya cancanci a yabawa kasar Ghana, domin manyan ‘yan kasuwa a Afirka, irin su Dangote da sauransu sun nuna cewa, samun bizar kasashen turai ya fi na Afirka sauki.

Ya kara da cewa, a harkar diflomasiya, duk wanda za a ba shi biza yana biyan kudi, amma kuma shugabannin Ghana sun jingine wannan mahimmancin samun kudin shigar, don karfafa alaka tsakanin kasashen Afirka. Ina gani ya kamata a yaba musu (wato yana nufin shugabannin Ghana) sosai.

Matakin ya samu karbuwa daga jamma'ar kasa r ta Ghana da masu sharhi da dama, kasancewar ana sa kyautata zaton matakin zai bunkasa harkokin kasuwanci, yawon bude ido, da musayar al'adu a fadin nahiyar Afirka.

A latsa na don a saurari rahoton Idris Abdallah Bako:

A baya, Ghana tana baiwa 'yan kasashen Afirka 26 izinin shiga ba tare da biza ba, sai kasashe 25 ana ba su biza yayin da matafiya suka iso kasar. Abubakar Garba Osman yace idan aka yi la’akari da yawan al’ummar Afirka, Ghana za ta amfana da wannan manufa, a bangaren tattalin arziki da yawon bude ido. Yace, ‘idan aka dubi yawan mutanen afirka biliyan daya da rabi. Idan ka duba kudin da Afirka ke samu a bangaren yawon bude ido, shi ne biliyan dari da tamanin da shida. Ka ga idan Ghana ta bude kofarta ga mutane, ka ga kasonta zai karu’.

Sai dai masani kan harkokin tsaro, Anas Seidu Sandow, ya ce duk da muhimmancin da matakin yake da shi ta bangaren tattalin arziki, amma zai baiwa ‘yan ta’adda kafar shiga kasar. Don haka, tilas ne jami’an tsaro, hukumar shige da fice, hukumar kwastan da sauransu, su binciki duk wadanda za su shigo kasar.

Ghana ta bi sahun kasashen Rwanda, Seychelles, Gambiya, da Benin a matsayin kasashen Afirka da suka ba da izinin shiga kasashensu ba tare da biza ba, ga duk masu rike da fasfon Afirka. A saurari cikaken rahoton Idris Abdalla:

VISA FREE FOR AFRICANS.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:51 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG