Shugaba Joe Biden na Amurka ya sanar da tawagar shugaban kasa ta musamman da za ta halarci bikin rantsar da Shugaba John Dramani Mahama na Ghana a ranar 7 ga watan Janairun da muke ciki, a birnin Accra, na kasar Ghana.
Shugaban hukumar gudanarwa da kasafi na Amurka, Shalanda D. Young ce za ta jagoranci tawagar.
Mambobin tawagar sun hada da jakadiyar Amurka a kasar Ghana, Virginia E. Palmer da magajin garin Los Angeles na jihar California, Karen Bass, da mashawarcin shugaban kasa na musamman kuma babban darakta akan al’amuran afrika da kwamitin tsaron kasa da kuma fadar White House, Frances Z. Brown.
Dandalin Mu Tattauna