Ma'aikatar ministan tsaron kasar Nijar ta rattaba hannu da WAPCO - Nijar, daya daga cikin rashen kamfanin man kasar China, domin bada tsaro da kariya na kayan aikin man kasar, da cewa yarjejeniyar tsakanin kasashen biyu za ta amfanesu wajen samun fetur danye da jigilarsa
Alamomin cutar sun hada da zazzabi, ciwon jiki, amai da gudawa, wadanda a wasu lokuta kan kai ga mutuwa.
Kura ta fara tashi game da yadda aka kashe wasu makudan kudade a Ghana kan Babbar Majami'ar Kasa (National Cathedral).
A cewar masu sharhi, wannan doka ba ta shafi 'yan kasashen da suka fito daga yankin kasashen ECOWAS ba.
Ma’aikatan da suka yi ritaya a Nijar sun koka a game da tsaikon da suka ce ana fuskanta wajen biyansu kudaden fansho, inda a yanzu haka wasu daga cikin irin wadanan tsofafin ma’aikata suka shafe watanni 10 ba tare da samun fansho ba
Ofishin jakadancin Amurka a Jamhuriyar Benin ya ba da sanarwar faduwar wani jirgi farar hula mai saukar ungulu, wanda rundunar sojan Amurka a nahiyar Afirka ta AFRICOM ke amfani da shi, domin ayyukan hadin gwiwa da dakarun kasar ta Benin a fannin kiwon lafiya.
A dajin Park W musamman wajen kan iyakokin kasashen Nijar, Benin da Burkina Faso ne ‘yan ta'adda suka afkawa daya daga cikin sansanonin soja mafi kunshe da kayan yaki na zamani na kasar Benin, inda suka hallaka sojoji da dama suka kuma arce da kayan aikinsu.
Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta bayyana shirin gudanar da bincike a matatar hadin gwiwar kasar da China wato SORAZ domin tantance abubuwan da suka wakana shekaru sama da 10 bayan kaddamar da ayyukanta
China na ci gaba da kokarin abota da kasashen Afurka saboda arzikin ma'adinai da nahiyar ke da shi.
Chadi da Senegal sun maida martani da kakausan murya bayan da Shugaba Macron ya bayyana cewa Faransa ce ta yi niyar kwashe sojojinta daga Afirka sabanin yadda ake ta shailar cewa korarsu aka yi daga nahiyar
Domin Kari
No media source currently available