washington dc —
A yau, Juma'a shugaban Ghana mai barin gado Nana Akuffo Addo ya gabatar da jawabinsa na ban kwana ga alu’mmar kasar.
Jawabin nasa na cike da alfahari kan kokarin da ya ce ya yi duk da kalubalen da kasar ta shiga a cikin wa’adinsa da suka hada da barkewar cutar annobar corona da ma yakin Ukraine da Rasha.
Shugaba Nana Addo ya ce zai bar Ghana fiye da yadda ya same ta sai dai babban jam’iyyar NDC mai adawa ta musanta hakan.
Saurari cikakken rahoton Hamza Adam daga Kumasi:
Dandalin Mu Tattauna