Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabuwar Shekarar 2025: 'Yan Nijar Sun Bayyana Fatansu


Shagulgulan Sabuwar Shekara
Shagulgulan Sabuwar Shekara

Tun saura kiris a shiga sabuwar shekara ta 2025 a Jamhuriyar Nijer ‘yan kasar ke bayyana fatan su game da kasar da ma mulkin sojan kasar a sabuwar shekara, ta la'akari da rayuwa mai tsada da suke fuskanta, da ma, yake yake da yan ta'adda da suka zagaye kasar.

Tun ana gap da shiga shekara ta 2025, a Jamhuriyar Nijer ‘yan kasar ke ta bitar yanayin da kasar take ciki, dauko daga tattalin arziki da rayuwa mai tsada da yan kasar ke fuskanta, uwa uba ma, maganar tsaro da ta yi ma kasar zobe, kasancewa gabas da yamma, kudu da arewa, yake yake ne kasar ke yi da yan ta'adda suka wa kasar zobe.

Jafaru Sarkin Shanu mai nazarin al'amuran kasa da kasa ne, yana cewa, kasar tana iya tsallake siradi, bayan kammala fita da ECOWAS a shekara ta 2025.

A cikin wannan lokacin ne, na bankwana da shekara ta 2024, wadansu yan Nijer suka bayyana kalubale, da ma tsadar rayuwar da suka fuskanta a wannan shekarar ta bana, duk da yake, suna masu cewa, alheri ya mayike musu daga baya.

Game da ko matsalar tsaro da ta gallabi ‘yan kasar matuka gaya, Liman Amadu ya soma da cewa, sakon shugaban kasar ta Nijer, shi ne, su cigaba da yin addu'o'i da saukar Alkur'ani Mai Tsarki, amma da sakin na mujiya idanu ga abinda ke kai komo a birane da kauyuka a wannan sabuwar shekara, yayin da sauran yan kasar ke neman Allah ya kawowa kasar Zaman lafiya.

Shekara dai mai kamawa ita ce, ta shirin ganin irin inda kasar zata dosa, a lokacin da zata cika shekaru biyu a hannun sojojin kasar.

Saurari cikakken rahoton Harouna Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG