Kasafin na bana ya tahallaka ne kan kudaden shiga na cikin gida a sakamakon matakin dakatar da tallafin da abokan hulda na kasa da kasa suka saba bayar wa a baya domin ayyukan ci gaban al’umma sanadiyar rigingimun da ke nasaba da juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Kasasfin wanda ya zarta na shekarar 2024 da kashi 4,13% ya zo da wasu sauye-sauyen da suka shafi sha’anin haraji da nufin farfado da tattalin arzikin kasa tare da bai wa al’umma damar samun kudaden shiga kamar yadda aka sanar a karshen taron majalissar ministoci na ranar 31 ga watan Disamba.
A karkashin wannan kasafi gwamnatin na hasashen samun kudaden shiga daga masu kasuwanci ta yanar gizo da masu fitar da kayayyakin noma da kiwo zuwa kasashen waje yayinda a wani bangare aka yi sassauci ga kananan ‘yan kasuwa da kamfanonin da ke fatan shigo da sabbin manyan motocin dakon kaya da na jigila.
Lamarin da shugaban kungiyar SIEN ta ‘yan kasuwar Import Export Alhaji Yacouba ‘Dan Maradi ke ganin zai samar da ci gaban kasuwanci da saukin farashi a kasuwanni.
A bisa al’ada Nijar kan samu kashi 40% na kudaden kasa da ya fi kowace shekara daga tallafin ketare to amma kasancewar abokan hulda na kasa da kasa sun jingine wannan tsari sakamakon rashin fahimtar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023 ya sa hukumomin kasar maida hankali wajen samar da dukkan kudaden da ake bukata daga cikin gida.
A jerin matakan sassaucin da gwamnatin ta Nijar ta dauka a bana an sassauta wa kafafen labaran masu zaman kansu harajin da suke biya a baya ganin yanayin matsin tattalin arzikin da wadanan kamfanoni ke fuskanta.
Fannin tsaro a nan cikin gida da ma ayyukan hadin guiwa a karkashin inuwar gamayyar AES da bunkasa ilimi da kiwon lafiya da gine-ginen hanyoyin mota na daga cikin ayyukan da ake saran bai wa fifiko a karkashin wannan kasafi a yayinda ake jiran samun kaso mai tsoka na kudaden da ake bukata daga fannin ma’adanan karkashin kasa.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna