A ranar Litinin ne dubban daliban Jami'ar Abdoul Moumouni Dioffo ta Yamai suka fito domin nuna rashin amincewarsu da yadda gwamnatin shugaba Mahamadou Issoufou ke tafiyar da ragamar mulki inda suka yi wata zanga zanga da ta yi sanadin mutuwar wani dalibi.
Dubban Daliban Jami'ar Abdoul Moumouni Dioffo Sun Yi Zanga-Zanga a Nijar

1
Dandazon daliban Jami'ar Abdoul Moumouni Dioffo yayin wata zanga zanga da suka yi. Ranar Litinin 10 ga watan Afirilu shekarar 2017.

2
Daya daga cikin shugaban kungiyar daliban zai yi jawabi a lokacin zanga zangar. Ranar Litinin 10 ga watan Afrilu 2017.

3
Jami'an tsaro akan tituna inda suka datse jerin gwanon dandazon daliban dake zanga zanga. Ranar Litinin 10 ga watan Afrilu shekarar 2017.

4
Shugaban Issoufou Mahamdou tare da gwamnatinsa, Yamai, Nijar