A wani taron gaggawa da suka yi a jihar Kaduna, Mr. Adewole ya ce yawancin wadanda cutar ta kashe yara ne daga shekara 5 zuwa 14.
Jami’an kiwon lafiya na gida da na waje sun gana da sarakunan gargajiya daga arewacin kasar don tattaunawa akan yadda za a shawo kan cutar a kuma magance ta, da yake sarakunan gargajiya daga arewacin kasar mutane ne masu tasiri sosai akan al’ummominsu. Mutane dayawa daga yankin sun fi yarda dasu akan jami’an gwamnati. Wadannan sarakunan sune ke kawarda duk wani champi ko rudani akan rigakafin cutar shan inna, suna kuma taimakawa wajen kawar da cutar a arewacin kasar.
An sami mutane fiye da 4,000 da suka kamu da cutar sankarau tun lokacin da cutar ta barke a cikin watan Disambar bara, kuma a yankin arewacin kasar mai fama da matsalar talauci cutar ta fi kamari.
Koda yake Cutar sankarau ba sabuwar cuta bace a Najeriya, amma wannan nau’in da ake kira C strain da turanci da ya bulla a yanzu, kusan sabon abune, a cewar shugaban hukumar yaki da cututtuka ta kasa, Dr. Chikwe Ihekweazu.
Facebook Forum