Kafafen yada labaran kasar China sun ce shugaba Xi Jinping ya fadawa shugaban Amurka Donald Trump cewa kamata yayi a warware rigimar da ake yi da Koriya ta arewa cikin lumana.
Rahotanni sun ce shugabannin biyu sun tattauna ne ta wayar tarho a yau Laraba, kusan mako daya bayan ganawar ido-da-ido da suka yi a taron kolin da suka yi a jihar Florida ta Amurka. Har yanzu dai fadar White House bata bada cikakken bayani kan tattaunawar da shugabannin biyu suka yi yau ta wayar tarho ba.
A jiya Talata, shugaba Trump yayi amfani da shafinsa na twitter don sake yin kira ga China akan ta taimaka wajen takawa Koriya ta arewa burki.
Facebook Forum