Ana tuhumar madugun ‘yan adawar kasar zambiya da laifin cin amanar kasa bayan da aka zarge shi da hana tawagar motocin shugaban kasar wucewa kwanan nan, a cewar rundunar ‘yan sandan kasar.
Shi dai Hakainde Hichilema, wanda ya ce bai amince da tsohon abokin adawarsa Edgar Lungu a matsayin shugaban kasa ba, da maraicen ranar litinin ne aka kama shi.
A lokacin da yake magana da manema labarai a birnin Lusaka, Babban jami’in ‘yan sanda, Kakoma Kakanja, ya tabattarda cewa lalle za’a tuhumi Hachilema da laifin zagon kasa.
A Zambia dai ba’a bada beli ga wadanda ake zargi da irin wannan laifin kuma laifi ne da za’a iya yanke wa mutum hukuncin kisa idan ya tabatta a kansa.
Facebook Forum