Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Dada Hada Kai Da Najeriya Ta Fuskar Tsaro


Shugaba Buhari Tare Da Shugaba Trump A Fadar White House
Shugaba Buhari Tare Da Shugaba Trump A Fadar White House

Da alamar su ma miyagun da ke gasa ma 'yan Najeriya aya a hannu sun kusa dandadawa, ganin yadda ake cigaba da kera ma Najeriya wasu jiragen yaki a Amurka, baya ga wasu matakan kuma da ake nazarin daukarsu.

Yayin da Najeriya ke dada fama da kalubalen tsaro, Amurka ta jadda kudirinta na kara hadin kai ta fannin tsaro da rundunar sojin Najeriya don shawo kan matsalar tsaro musammanma na masu tada kayar baya a shiyyar arewa maso gabas.

Sakatariyar Harkokin Sojojin Saman Amurka, Barbara Barret, wacce ta
ziyarci hedikwatar rundunar mayakan saman Najeriya a Abuja, bisa rakiyar
jakadiyar Amurka a Najeriya, Ambassador Mary Beth, ta ce alakar da za a
karfafa zata mayar da hankali ne kan fannonin samar da kayakin aiki
da jiragen yaki, horaswa da kuma bai wa dakarun saman Najeriyar wasu
damammaki.

Iya Mashal Abubakar, da Barbara Barret
Iya Mashal Abubakar, da Barbara Barret

Uwargida Barrett ta ce tabbatar da irin wannan alaka ya zama wajibi don kara yaukaka sha'anin kwarewa a farmakin sama da mayakan Najeriyar suke
kaiwa, tana mai cewa sun ji dadin yadda aka yi aiki tare a baya da fatan
za a ci baba da aiki tare nan gaba.

Amurka, inji Sakatariyar, na ganin kima da darajar sojojin saman
Najeriya ta yadda a baki dayan rundunonin sojojin saman Afurka ta fi
son yin alaka da kuma aiki tare da sojojin saman Najeriya.

Iya Mashal Abubakar, Barbara Barret da Jakadiya Mary Beth
Iya Mashal Abubakar, Barbara Barret da Jakadiya Mary Beth

Ta ce Amurka na sane da irin kalubalen tsaro da ke fuskantar Najeriya
musamman ma a arewa maso gabas don haka tana mai tabbatarwa rundunar sojin saman kasar goyon baya.

Sakatariyar harkokin sojin saman Amurkan ta tabbatar wa rundunar
mayakan saman Najeriyar cewa Amurka zata jibanci al'amarinta ganin
yadda take abubuwanta bisa tsari kamar yadda ya kamata

Tunda farko, sai da babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya, Air
Marshall sadique Abubakar, ya bayyana ziyarar wannan babbar jami'a a
matsayin wani kyakkyawan al'amarin da ke nuna irin dasawar dake
tsakani, yana mai cewa Amurka ta taka muhimmiyar rawa wajen nasarar
da ake samu a filin daga, ganin da dama daga cikin dakarunsa a Amurkar aka horas dasu.

Tawagar Iya Mashal Abubakar, Barbara Barret, da Ambassador Mary Beth
Tawagar Iya Mashal Abubakar, Barbara Barret, da Ambassador Mary Beth

Air Marshall sadique Abubakar ya ce ana samun cigaba kan batun manyan
jiragen yakinnan na zamani wato A29-SUPER TUCANO da Najeriya ta yi oda daga Amurkar, ganin yanzu haka wasu dakarun sojin saman Najeriyar na can Amurkan na sa ido kan yadda ake kera jiragen kuma duk sati suna
turo da rahoton halin da ake ciki na irin nasarar da ake samu.

XS
SM
MD
LG