Ana dai zargin Trump ne da haddasa rikicin da ya faru a majalisar kasar, inda daruruwan magoya bayansa su ka hana majalaisar aikinta a ranar 6 ga watan nan.
A wani taro kusa da fadar White House, Trump ya nemi magoya bayansa da su yi tattaki zuwa majalisar kasar, su tunkari ‘yan majalisun, a dai-dai lokacin da suke muhawarar tabbatar da sakamakon zaben wakilan electoral College, da zai tabbatar da Biden a mastayin wanda aka zaba.
A makon da ya gabata ne dai aka rantsar da Biden a mastayin shugaban Amurka na 46.
Sanata Rubio, mai wakilatar jihar Florida, ya shaida wa gidan talabijin na Fox news jiya Lahadi cewa, “Duk da cewar Trump na da alhakin laifin wasu daga cikin abun da suka faru, amma shi bai yadda da shari’ar da majalisar dattawan zata yi ba, biyo bayan tsige shi da majalisar wakilai ta yi.”
Arangamar dai ta kai ga rasuwar mutane 5, da ya hada da dansanda 1, wanda ake cigaba da bincike akan mutuwarsa. Magoya bayan Trump sama da 800 ne suka abka wa ‘yan sanda, suka shiga majalisar suka farfasa gilasai da sauran kaya, a cewar mahukunta, daga baya dai an samu damar shawo kansu, kuma ‘yan majalisun suka cigaba da aikinsu na tabbatar da nasara ga Biden a ranar 7 ga wata.
“Zamu sake komawa cikin abun da muka tsinci kanmu shekaru 5 da suka wuce, sake bincike wanda bai da wani alfanu ga kasar.” A cewar Rubio.
Ya kara da cewar “Wannan ba binciken babban laifi bane, siyasa ce kawai, kuma zata kara rarraba kan kasar.”