Suna masu dora laifin abun da ya faru a ranar Laraba a kansa, wanda yayi sanadin mutuwar mutum 5 a majalisar kasar. Inda magoya bayansa da ke bore suka doke ‘yan sanda suka abka cikin ginin majalisar.
Babu wata matsaya da a ka cimma, amma da yiwuwar kakakin majalisar, Nancy Pelosi, ta gabatar da tuhumar zarginsa da haddasa rikicin, da ya faru a majalisar lokacin da suke kokarin tabbatar da zabe kamar yadda wakilan Electoral College su ka gabatar, na tabbatar da Biden a matsayin Shugaban kasa.
Biden dai bai saka hannunsa a cikin dambarwar tsige Shugaban mai barin gado ba, wanda har ya zuwa yanzu bai aminta da cewar ya fadi zaben ba. Duk kuwa da cewar Trump ya aminta da cewar za a rantsar da “sabuwar gwamnati” a birnin gundunar Kwalambiya a ranar 20 ga watan Janairu.
"Nan da kwanaki 10, zamu fuskanci abun da ke gaban mu na gina kasa tare" a cewar Biden jiya Lahadi ta kafar twitter.
Daya daga cikin makusanta Pelosi, dan majalisa mai wakiltar South Carolina, Jim Clyburn, ya shaida wa gidan talabijin na Fox News jiya Lahadi cewar, “Da alamu ‘yan majalisar zasu gabatar da kudurin tsige Shugaban, nan da ‘yan kwanaki. Duk kuwa da cewar wa’adin mulkin shi zai kare nan da mako mai zuwa, kuma za a rantsar da Biden dadadden dan siyasar Amurka tare da Mataimakiyarsa Kamala Harris.