Jiya Lahadi an fara jigilar sabbin alluran rigakafin coronavirus ta jiragen sama daga kamfanin hada magunguna na Pfizer dake garin Kalamazoo, na jihar Michigan, zuwa sassa da yankunan kasar Amurka.
Yayin da kasashe ke amincewa da riga kafin coronavirus, ana ci gaba da samun bukatar gaggawa ta bada riga kafin yayin da kuma ake samun adadin tarihi na masu kamuwa da cutar da kuma mace-mace a kasashe da yawa.
Amurka ta tabbatar da bukatar gaggawa na afmani da maganin rigakafin coronavirus kana maganin zai fara isa ga mutane da safiyar gobe Litinin a fadin Amurka.
Jiya Juma’a shugaban ma’aikatan fadar shugaban Amurka, Mark Meadows ya matsawa shugaban hukumar abinci da magani Stephen Hahn lamba da ya amince da bukatar gaggawa ya bada izinin amfani da rigakafin coronavirus da kamfanin Pfizer ya yi kafin karshen wuni ko kuma a kore shi bakin aiki, inji jami'ai.
Kafafen yada labaran Amurka sun ce shugaba Joe Biden mai jiran gado zai nada Marcia Fudge, ‘yar majalisar wakilai daga jam’iyyar Democrat a matsayin sakatariyar kula da harkokin samar da gidaje da raya birane.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kai ziyara a jihar Georgia da ake kallonta mai muhimmanci a ranar Asabar domin gudanar da gangamin siyasa tare da ‘yan takarar majalisar dattawa na Republic wanda zasu fafata da ‘yan Democrat a zaben zagaye na biyu a watan Janairu,
Ma’aikatar tsaron Pentagon ta Amurka ta fada a jiya Juma’a cewa za ta janye yawancin dakarun Amurka daga Somalia bisa umurnin shugaba Donald Trump, da ke ci gaba da kokarin rage shiga harkokin yaki da ta’addanci da Amurka ke yi a kasashen ketare bayan zaben kasar da aka yi.
Zababben shugaban Amurka Joe Biden ya yi hasashen ganin makoma mai tattare da kalubaloli, idan majalisun kasar basu gaggauta daukar mataki a kan kudirin tallafin coronavirus, yayin da cutar ke kara ta’azzara a fadin kasar, lamarin dake kawo cikas ga farfadowar kasar.
Kasar Birtaniya ta bada amincewar gaggawa akan fara amfani da sabon riga kafin COVID-19 da babban kamfani Pfizer da ke Amurka ya hada.
Wannan na zuwa ne yayin da Joe Biden ya damka wa mata sashen sadarwar fadar White House
Zababben shugaban Amurka, Joe Biden da Mataimakiyar Shugaban mai jiran gado Kamala Harris, sun sanar da nadin tawagar mata zalla a fannin sadarwa.
A jiya Juma’a Amurka ta sanar da aza takunkumai a kan wasu kamfanonin China da Rasha da Washington ta ce suna taimakawa shirin kera makamai masu lizzami na Iran.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.