Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Trump Ta Bada Umurnin Janye Dakarun Amurka a Somalia


Ma’aikatar tsaron Pentagon ta Amurka ta fada a jiya Juma’a cewa za ta janye yawancin dakarun Amurka daga Somalia bisa umurnin shugaba Donald Trump, da ke ci gaba da kokarin rage shiga harkokin yaki da ta’addanci da Amurka ke yi a kasashen ketare bayan zaben kasar da aka yi.

Ba tare da bada cikakken bayani ba, ma’aikatar ta Pentagon ta fada a wata ‘yar takaitacciyar sanarwa cewa “za a kwashe galibin” dakarun Amurka da kaddarori a Somalia zuwa farkon shekarar 2021.

Akwai kimanin sojoji 700 a kasar da ke gabashin Afrika, wadanda ke bada horo da shawarwari ga sojojin Somalia a ci gaba da yakin da su ke yi da kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta al-Shabab, mai alaka da al-Qaida.

A kwanan nan Trump ya bada umurnin a rage yawan dakarun Amurka da ke Afghanistan da Iraq, kuma ya na sa ran janye wasu ko ma dukkan dakarun kasar da ke Somalia. Janar Mark Milley, shugaban hadakar manyan hafsoshin kasashen, ya fada a ranar Laraba cewa har yanzu ana kan yin muhawara game da makomar yawan sojojin Amurka a Somalia.

Matakin janye dakarun na Amurka daga Somalia da shugaba Donald Trump ya dauka yayin da kwanakinsa a matsayin shugaban kasa suka kusa karewa ya janyo bacin rai sosai daga ‘yan Somalia, wadanda a yau Asabar suka roki shugaba mai jiran gado ya sauya matakin.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG