Zaben dai shine zai tabbatar da jami’iyar da zata samu rinjayi a majalisar dattatawa da zata yi aiki da gwamnatin Joe Biden.
Biden, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya lashe jihar Georgia amma ba a sanar hukumance ba da tazaran kuru’u kusan dubu 12 acikin kimanin kuru’u miliyan biyar da aka kada. Amma kwamitin yakin neman zaben Trump ya ce ya shigar da kara a kotu a ranar Juma’a domin kotun ta soke sakamakon zaben na ranar uku ga watan Nuwamba a jihar.
Trump dan Republican, ya je Georgia ne domin ci gaba da gangamin bayan zabe na neman soke nasarar da Biden dan Democrat ya yi a jihar da ma wasu muhimman jihohi da ake kwatantawa da fagen daga kana ya kalubalanci sakamakon zaben na kasa baki daya.
A jiya Asabar, Trump ya yi kira ga gwamnan jihar Georgia Brian Kemp, da ya shirya wani taro na musammab da ‘yan majalisar jihar domin su soke sakamakon zaben da aka yi a jihar kana su zabi masu gudanar da zabe da zasu goyi bayansa, a cewar jaridar The Washington Post. Fadar White taki cewa uffan a kan wannan batu.
Jami’iyar Republican na bukatar Karin kujeru domin ta ci gaba da rike rinjayi a majalisar dattawan Amurka. Dan majalisa na Republican David Perdue na bukatar ya doke Jon Ossoff a ranar biyar ga watan Janairu a zagaye na biyu, yayin da Sanata Kelly Loeffer na Republican shima yake bukatar doke abokin karawarsa, Raphael Warnock.
Idan ‘Yan takarar Republican suka fadi a zaben, bangarorin biyu zasu tashi da kujeru 50-50 a majalisar dattawa, inda mataimakiyar shugaban kasa Kamala Haris zata kada kuri’a da zata raba gardama.