"Sadarwa kai tsaye ta gaskiya ga jama'ar Amurka na daya daga cikin mahimman ayyukan shugaban kasa, kuma za a damka wa wannan tawaga babban nauyin hada Amurkawa da Fadar White House," a cewar Biden cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai. daga ofishin kwamitin karbar mulki.
Ya kara da cewa "Wadannan kwararrun masana sadarwa suna kawo ra'ayoyi daban-daban ga aikinsu da kuma sadaukar da kai, don gina kasar nan da kyau."
Kate Bedingfield, wacce ta yi aiki a matsayin darektar sadarwa na yakin neman zaben Biden-Harris, an nada ta daraktar sadarwa ta Fadar White House.
Ita kuma, Pili Tobar, wacce ta yi aiki a matsayin mataimakiyar darakta a kungiyar Muryar Amurkawa, wata kungiya mai rajin kawo sauyi kan shige da fice, za ta zama mataimakiyarta.
Sai kuma, Ashley Etienne, wacce ta yi aiki a matsayin darektar sadarwa ta Kakakin Majalisa Nancy Pelosi, an nada ta a matsayin daraktar sadarwa ta Harris.