Birtaniya ce ta zama kasa ta farko a yammacin duniya da ta shirya fara bada riga kafin cutar da ta kama kusan mutane miliyan 64 a fadin duniya, ciki har da mace-mace miliyan 1.4.
Ranar Laraba 2 ga watan Disamba ne hukumar kula da magunguna ta kasar ta bada izinin fara amfani da riga kafin, wanda kamfanin magungunan Pfizer ya hada tare da kamfanin BioNtech na Jamus. A mako mai zuwa ne za a fara bada riga kafin, kuma ana sa ran jami’an kiwon lafiyar Birtaniya da masu kula da marasa lafiya a cibiyoyi za a ba muhimmanci wajen raba riga kafin.
A Amurka kuma, ma’aikatan jinya da jami’an da ke aiki a cibiyoyin da ake kula da marasa lafiya ya kamata su kasance kashin farko na Amurkawa da za a ba riga kafin COVID-19, matakin da mambobin kwamitin bada shawara na cibiyar kula da cututtuka masu yaduwa ta Amurka da ake kira CDC suka cimma kenan ranar Talata 1 ga watan Disamba.
Mambobin kwamitin 13 ne suka kada kuri’ar amincewa da bada riga kafin ga kusan ma’aikatan jinyar Amurka ko kuma masu aiki a cibiyoyin da ake kula da marasa lafiya miliyan 24, da zarar an amince da shi, mutun daya kuma ya yi akasin haka, yayin da har yanzu ake fuskantar karancin kayayyakin aiki yayin da kuma ake kara yawan kayayyakin da ake sarrafawa.
Matakin kwamitin bada shawarar na CDC akan harkokin allurar riga kafin na zuwa ne yayin da Amurka ta samu adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 na tarihi. Mutane miliyan 4.36 da aka sani ne suka kamu da COVID-19 a watan Nuwamba a Amurka, adadin da ya kusan linka wanda aka samu a watan Oktoba.
A jiya Talata adadin da aka samu na wadanda suka kamu da cutar a jihar Florida ya zarta miliyan 1.