Ranar Litinin 30 ga watan Nuwamba zababben Shugaban Amurka Joe Biden zai fara karbar bayanan da ake bai wa shugaban kasa a kullum, abin da zai ba shi damar samun rahotannin da hukumomin tattara bayanan sirri ke shiryawa kan batutuwan da suka shafi tsaron kasa yayin da ya ke shirin kama aiki a watan Janairu.
Hakazalika a ranar Litinin din ake sa ran Biden da zababbiyar mataimakiyarsa Kamala Harris za su bayyana sunayen mutanen da za su rike manyan mukamai a fannin tattalin arzikin kasar a gwammatinsu.
Kafofin watsa labarai da dama, bisa ga bayanai daga mutanen da ke da masaniya game da tsarin, sun ba da rahoton cewa, Neera Tanden ita ce za ta jagoranci ofishin kasafin kudi a fadar White House, tare da masaniyar tattalin arziki Cecilia Rouse wacce za ta zama shugabar majalisar masu ba da shawara kan tattalin arziki.
Ranar Lahadi 29 ga watan Nuwamba ne Shugaban mai jiran gado da mataimakiyarsa suka sanar da sunayen matan da aka danka wa sashen sadarwar fadar White House.