Maganin rigakafin da Pfizer da takwararsa na kasar Jamus BioNTech suka yi, ya samu amince ainun a ranar Alhamis daga kwamitin mashawartar hukumar abinci da magani na kasar waje kana ana sa ran hukumar zata kammala aiki a cikin ‘yan kwanaki, yayin da mataki na gaba da ake sa ran gani shine amfani da maganin.
Ba lallai bane hukumar ta FDA ta yi aiki da kowace shawarar da kwamitocinta zasu bata, amma galibi hakan ke faruwa.
Meadows ya yi magana da Hahn ta waya a jiya Juma’a, a cewar wani babban jami’in gwamnatin wanda ya ji tattaunawar su amma ba a bashi damar bayyana hirar da aka yi cikin sirri ba.
Shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasar ya fadawa Han cewa akwai yiwuwar rasa aikin sa idan bai amince da buakatar gaggawa kafin yau Asabar ba, inji jami’i na biyu da shima ya ji tattaunawar.
Hahn ya ce zai ba masu kula da sha’anin magunguna izinin amincewa da maganin rigakafin a kan matsayi na gaggawa, a cewar jami’in.
Tun da safiyar jiya Juma’ar ce shugaba Doanld Trump ya yita matsawa a tabbatar da maganin a wani sakon tweeter da ya fitar kai tsaye a kan Hahn, yana mai cewa hukumar FDA wani katon tsohon kunkuru ne mai sanyi jiki. Trump ya caccaki yanda FDA ke tafiyar hawainiya wurin tabbatar da maganin rigakafin.