Kamfanonin hudu da aka zarginsu da yin musayar muhimman fasahohi da kayan aiki ga shirin kera makaman Iran, zasu huskanci takunkumai a kan taimakon gwamnatin Amurka da suke samu wurin aikewa da kaya tsawon shekaru biyu, inji skataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo.
Ma’aikatun da aka dora musu takunkuman a ranar Laraba, sun hada ne da kamfanonin China guda biyu, Chengdu Best New Materials da Zibo Elim Trade da na Rahsa biyu da su kuma suka hada da Nilco Group da Joint Stock Company Elecom.
Pompeo yace zasu ci gaba da takawa shirin makaman Iran burki kana zasu sa hukumomi su lura da ‘yan kasar waje da zasu kaiwa Iran kaya kamar irin wadannan kamfanoni na China da Rasha.
A shekarar 2018, shugaba Donald Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka kulla shekaru uku a waccan lokacin karkashin shugaban Barack Obama.
Trump ya riga ya dora takunkumai masu tsauri a kan Jamhuriyar Islamiyar a wani mataki da ya kira gangamin kara matsin lamba.
Haka zalika gwamnatin Trump ta bayyana aniyarta na aza takunkumi a kan duk wata kasar waje ko kamfani da bai yi biyayya ga manufofinta a kan kasar Iran.