Shugaban tawagar ‘yan wasan kasar Iraqi ya ce shugabannin Olympics sun yi watsi da bukatar su cewa kada a cira tutar Isra’ila a kusa da ta Iraqi a lokacin wasannin Paris.
Yau Asabar ma’aikatar tsaron Isra’ila ta bada umarni kwashe mutane daga wani wuri mai tarin jama’a a Gaza inda aka kebe domin gudanar da ayyukan jin kai.
Hukumar wasannin Olympics ta kasa da kasa ta nemi afuwa a ranar Asabar dangane da wani kuskure da aka tafka a yayin bikin bude gasar wasannin Olympics a birnin Paris, inda aka yi kuskuren gabatar da 'yan wasan Koriya ta Kudu a matsayin na Koriya ta Arewa.
A yau Juma’a za a bude gasar wasannin Olympics ta shekarar 2024 a hukumance, inda 'yan wasa sama da 10,000 zasu hallara a birnin Paris, suna fatan lashe lambar yabon zinariya, azurfa ko tagulla.
‘Yan sanda a Nepal sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, wani jirgin saman fasinja ya rikito yayin da yake kokarin tashi a babban birnin kasar, Kathmandu, inda aka yi nasarar ceto matukin daga tarkacen jirgin dake ci da wuta, saidai dukkanin mutane 18 din dake cikin jirgin sun hallaka
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai samu tarba daga ‘yan Majalisar Dokokin Amurka dake fama da mummunan rabuwar kai da al’ummar kasar da suka shagaltu da wasu al’amura da kuma gagarumin gangamin zanga-zanga a yau Laraba yayin gabatar da jawabi gaban majalisar a karo na 4 a tarihi
A jiya Litinin Wani kwararre a Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci a gudanar da binciken kasa da kasa kan "laifin cin zarafi da zalunci," da suka hada da kisan kiyashi kan 'yan tsiraru addinai da kuma kisan kare dangi ga 'yan adawa a shekarar 1980 da aka aikata a Iran.
A yau Lahadi Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar a cikin wata wasika da ya aikewa al'ummar kasar cewa ba zai sake tsayawa takara ba kuma ya dakatar da yakin neman shugabancin kasar da yake yi ta bana.
Kasar Pakistan ta yi Allah wadai da gazawar kasar Jamus na kare karamin ofishin jakadancinta a Frankfurt da aka bayar da rahoton cewa wasu masu zanga zanga dauke da tutar kasar Afghanistan suka kutsa kai tare da lalata ofishin a ranar Asabar.
Biyo bayan wani mummunan hari da mayakan Houthi su ka kai a birnin Tel Aviv a kwanan nan, Isra'ila ta kai wa 'yan tawayen hari a Yemen har mutane uku suka mutu.
Sannu a hankali layukan internet na kamfanonin jiragen sama sun fara dawowa yau Asabar bayan da kamfanonin sadarwa na duniya, da bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi suka fada cikin rudani sakamakon gagarumar katsewar layukan internet a cikin 'yan shekarun nan, don aikin sabunta matakin kariya.
An kashe akalla mutane 13 a wasu hare-hare uku da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijira da ke tsakiyar Gaza cikin dare zuwa yau Asabar, a cewar jami’an kiwon lafiyar Falasdinu, yayin da ake ganin ana samun ci gaba a tattaunawar tsagaita bude wuta a birnin Alkahira.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.