Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Joe Biden Ya Janye Daga Takarar Shugabancin Amurka


Shugaban Amurka Joe Biden Yayin Da Yake Jawabi Ga Al'ummar Amurka
Shugaban Amurka Joe Biden Yayin Da Yake Jawabi Ga Al'ummar Amurka

A yau Lahadi Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar a cikin wata wasika da ya aikewa al'ummar kasar cewa ba zai sake tsayawa takara ba kuma ya dakatar da yakin neman shugabancin kasar da yake yi ta bana.

Biden ya bayyana a cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X cewa, "duk da cewa nayi niyar sake yin takara, sai dai ina da yakinin cewar abinda yafi dacewa ga jam'iyyata da ma kasa baki daya shi ne in janye daga takarar tare da mayar da hankali kan kammala ragowar wa'adin mulkina."

Biden ya kara da cewa, nan gaba kadan zai yi wa al'ummar Amurka cikakken jawabi akan lamarin.

Yanzu dai shugaba Biden ya tabbatar da amincewarsa ga mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ta maye gurbinsa.

Sai dai an tsara gudanar da babban taron jam'iyyar Democrat na bana, inda a hukumance za'a fidda wanda zai yiwa jam'iyyar takara a tsakanin ranakun 19 zuwa 22 ga watan Agusta mai kamawa a birnin Chicago.

Hakan ya biyo bayan damuwa da wasu ‘yan Democrat suka bayyana game da yadda masu kada kuri’a ke jefa ayar tambaya kan shekarun Biden da kuma damar samun galaba kan Trump a zabe mai zuwa idan ba a yi sauyi ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG