Sai dai daga cikin su har da mata da yawa daga kasashen Afirka, wadanda da yawansu su ka jure wa kalubale da yawa don zuwa Paris.
A karon farko a tarihi, kwamitin wasannin Olympic na duniya, da ake kira IOC, ya bayyana cewa an samu cikakken daidaiton jinsi a fagen wasan gasar Olympics ta bana.
Mata 'yan wasa, wadanda a baya suka kasance kusan kashi 2 cikin 100 na masu fafatawa a gasar Olympics, a yanzu kusan yawan su daya da maza.
Mata ne kashi 48 cikin 100 na ‘yan wasan gasar Olympics da aka yi a Tokyo shekaru uku da suka wuce, wanda aka jinkirta da shekara daya saboda annobar COVID-19.
Matan Afirka da dama na daga cikin wadanda za su fafata a gasar.
Esti Olivier ‘yar wasan tseren kwale-kwale ce, daya daga cikin masu wakiltar Afirka ta Kudu.
A karon farko za ta fafata a gasar Olympics bayan da ta rasa damar zuwa wasannin Tokyo saboda rashin lafiya da ta fuskanta.
Dandalin Mu Tattauna