Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Tana Shirin Kai Farmaki A Wani Sansanin 'Yan Gudun Hijira A Gaza

Israeli army troops stand around their tanks in an area along the border with the Gaza Strip in southern Israel on April 10, 2024, amid the ongoing conflict in the Palestinian territory between Israel and the militant group Hamas. (Photo by JACK GUEZ / AF

Yau Asabar ma’aikatar tsaron Isra’ila ta bada umarni kwashe mutane daga wani wuri mai tarin jama’a a Gaza inda aka kebe domin gudanar da ayyukan jin kai.

Ma'aikatar ta fada cewa tana shirin kai farmaki a kan mayakan Hamas a Khan Younis, da wani bangaren Muwasi da aka tsugunar da dubban ‘yan gudun hijira.

Umarnin ya biyo bayan martani da Isra’ila ta bayar kan wani makamin roka da ta ce an harbo ne daga wurin.

Umarnin kwashe mutanen shine na biyu a cikin mako guda daga wurin da aka kebewa Falasdinawa da suka tsere daga wasu sassan Gaza. Sau tari ana tada Falasdinawa da dama da suke neman mafaka daga farmaki ta sama da kasa da Isra’ila ke kaiwa.

Displaced Palestinians gather in the yard of Gaza's Al-Shifa hospital on December 10, 2023, as battles continue between Israel and the militant group Hamas in the Palestinian territory.
Displaced Palestinians gather in the yard of Gaza's Al-Shifa hospital on December 10, 2023, as battles continue between Israel and the militant group Hamas in the Palestinian territory.

A ranar Litinin jim kadan bayan umarnin tada mutanen, hare hare da dama da Isra’ila ta kai ta sama a gewayen Khan Younis ya kashe akalla mutane 70, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza, tana nuni da wasu alkallumar da asibitin Nasser ya fitar.

Wannan bangaren yana cikin yanki mai girmar murabba’in kilomita 60 wanda aka kebe domin gudanar da ayyukan jin kai, wanda Isra’ila ta yita fadawa Falasdinawa su tashi daga wurin tun farkon yakin.

Gaza
Gaza

An yi amfani da wani bangare mai girma na yankin aka kafa dakunan tanti wanda ba su da kayayyakin tsafta kana ba asibitotci sannan ba su samun isasshen taimakon jin kai, a cewar MDD da kungiyoyin jin kan.

Kimanin Falasdinawa miliyan guda da dubu 800 ne suke tsugune a wurin a cewar wani kiyasin Isra’ila. Wannan adadin ya kai rabin al’ummar Gaza, mai mutane miliyan 2 da dubu 300 kafin yakin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG