Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sama Da Mutum 670 Sun Mutu Sakamakon Zaftarewar Kasa A Papua New Guinea - MDD


Papua New Guinea - Zaftarewar kasa
Papua New Guinea - Zaftarewar kasa

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta kasa da kasa a ranar Lahadi ta kara kiyasin adadin mutanen da suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a Papua New Guinea zuwa sama da 670 yayin da masu ba da agajin gaggawa da ‘yan’uwansu suka yi fatali da fatan cewa za a sake samun wanda suka tsira.

WASHINGTON, D. C. - Serhan Aktoprak, babban jami’in hukumar kula da shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya a tsibirin Kudancin na Pacific, ya ce adadin wadanda suka mutu da aka yi wa kwaskwarima ya samo asali ne daga lissafin da kauyen Yambali da jami’an lardin Enga suka yi cewa sama da gidaje 150 ne aka binne sakamakon zaftarewar kasa a ranar Juma’a. Amma kididdigar da ta gabata ta kasance gidaje 60 ne.

Papua New Guinea, Mayu 24, 2024.
Papua New Guinea, Mayu 24, 2024.

"Suna kiyasta cewa fiye da mutum 670 ne a karkashin kasa a halin yanzu," Aktoprak ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press.

Da farko dai jami’an yankin sun sanya adadin wadanda suka mutu a ranar Juma’a ya kai 100 ko sama da haka. Gawarwaki biyar ne kawai da kafa na mutum na shida da aka samu a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da wani injin din tono da wani magini ya bayar da taimako, ya zama na farko na na'urorin motsa kasa don shiga aikin farfadowa.

Ma’aikatan agaji sun yi ta kwashe wadanda suka tsira zuwa kasa mai tsaro a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da dimbin kasar da ke fama da rashin kwanciyar hankali da yakin kabilanci, da ke yaduwa a tsaunukan Papua New Guinea, suka yi barazana ga yunkurin ceton.

Papua New Guinea
Papua New Guinea

Kimanin karin gidaje 250 suka lalace gaba daya tun bayan zaftarewar kasa saboda har yanzu kasar na ci gaba da motsi, inda aka kiyasta mutum 1,250 suka rasa matsuguni, in ji jami'ai.

A halin da ake ciki gwamnatin kasar na nazarin ko za ta bukatar neman karin tallafi na kasa da kasa a hukumance.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG