Isra'ila za ta karbe iko a Rafah ko da kuwa zai haifar da baraka da Amurka, in ji wani babban jami'in Isra'ila a ranar Alhamis, yana mai bayyana birnin Gaza mai cike da 'yan gudun hijira a matsayin sansanin karshe na Hamas mai dauke da kashi daya bisa hudu na mayakan kungiyar.
A ranar Alhamis ne wani jirgin ruwa na kasar Indonesiya ya gano wani kwale-kwalen katako da ya kife da ‘yan gudun hijira Musulman Rohingya da dama, suka kuma ceto wadanda suka tsira da rayukansu da ke tsaye a kan katakon jirgin.
Hukumomi a Pakistan sun ce a ranar Laraba mutane 6 galibi jami'an tsaro ne suka mutu a lokacin da wasu gungun 'yan ta'adda dauke da muggan makamai suka kai hari a wani ginin gwamnati a birnin Gwadar da ke kudu maso yammacin kasar, garin da ke da wata tashar jiragen ruwa mallakar kasar China.
Zaman dardar ya karu yayin da shugaban Hamas ya zargi Isra'ila a ranar Talata da yin zagon kasa ga tattaunawar ake yi ta tsagaita bude wuta a Gaza bayan da, a karo na biyu, Isra’ilar ta kai farmaki a asibiti mafi girma a yankin Falasdinu da ya daidaice.
‘Yan sandan Brazil sun ba da shawarar a tuhumi tsohon shugaban kasar, Jair Bolsonaro, kan zargin yin jabun takardar shaidar rigakafinsa na Covid, a cewar wani rahoton bincike da aka buga ranar Talata.
Yawancin asibitoci a kasar China sun daina ba da kulawar haihuwa ga jarirai a bana, kamar yadda wata kafar yada labarai ta Daily Economic News ta bayar da rahoton, inda kwararrun masana suka yi gargadin "raguwar haihuwa" saboda raguwar bukatu a yayin da ake samun raguwar sabbin haihuwa.
Wadansu 'yan kasar Rasha da Ukraine sun bayyana nasarar zaben Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a karo na shida a matsayin koma baya, yayin da kasashen yammacin duniya ke Allah wadai da zaben.
Shugaban Rasha Vladimir Putin ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar da gagarumin rinjaye, lamarin da zai ba shi wani karin wa'adi na mulki.
Rikicin siyasa da karuwar tashe-tashen hankula a Haiti sun haifar da yanayi mai wahalar magancewa ga al'ummar Haiti.
A ci gaba da kwan gaba kwan baya da huldar Jamhuriyar Nijar da wasu kasashen Yamma ke yi, kasar da ke karkashin mulkin soji, ta yi shelar yanke huldar soji da Amurka.
Kungiyar agaji ta SOS Mediterranee a yau Alhamis ta ce, wasu da aka ceto daga wani jirgin ruwan roba da ya barke a tsakiyar tekun Mediterrenean, sun sanar da cewa, wasu mutane 50 da suka tashi daga kasar Libya tare da su mako guda da ya wuce sun halaka a cikin wannan tafiya.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.