Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Sha Alwashin Shiga Rafah Duk Da Cewa Matakin Zai Kawo Baraka Tsakaninta Da Amurka


Biden Netanyahu
Biden Netanyahu

Isra'ila za ta karbe iko a Rafah ko da kuwa zai haifar da baraka da Amurka, in ji wani babban jami'in Isra'ila a ranar Alhamis, yana mai bayyana birnin Gaza mai cike da 'yan gudun hijira a matsayin sansanin karshe na Hamas mai dauke da kashi daya bisa hudu na mayakan kungiyar.

WASHINGTON, D. C. - Hatsarin ganin tankokin yaki da dakaru da za su mamaye Rafah na damun Amurka idan babu wani shiri na kwashe Falasdinawa sama da miliyan daya da suka yi hijira zuwa wasu wurare a zirin Gaza a yakin da aka kwashe watanni biyar ana yi.

Firaminister Isra’ila Benjamin Netanyahu
Firaminister Isra’ila Benjamin Netanyahu

Firai Minista Benjamin Netanyahu ya yi alkawarin tabbatar da kwashe fararen hula da kuma bada agajin jin kai, matakan da manyan mataimakan Isra'ila za su tattauna a fadar White House a cikin kwanaki masu zuwa, bisa umarnin Shugaban Amurka Joe Biden.

"Muna da kwarin gwiwa cewa za mu iya yin hakan ta hanyar da za ta yi tasiri, ba kawai ta hanyar soji ba, har ma da bangaren jin kai. Amma kuma ba su da yardar cewa za mu iya yin hakan," daya daga cikin wasu jakadun Isra'ila, na Harkokin Dabaru Minista Ron Dermer, ya fadi haka a wani shiri na "Call Me Back da Dan Senor".

Dermer, wanda tsohon jakadan Amurka ne, ya ce Isra'ila za ta ji ra'ayoyin Amurka game da Rafah, amma za a shiga ta kwace birnin da ke kan iyakar Gaza da Masar ko kasashen kawancen sun cimma matsaya ko a'a.

Rafah
Rafah

"Hakan zai faru ko da an tilastawa Isra'ila yaki ita kadai, ko da duk duniya ta hau kan Isra'ila ciki har da Amurka, za mu yi yaki har sai an samu nasara."

Yayin da ake ci gaba da gwabza fada a arewacin Gaza, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya ziyarci birnin Alkahira domin tattaunawa da jami'an kasashen Larabawa game da shirin tsagaita wuta. Isra'ila a shirye take ta sasanta, amma ta yanke hukuncin kawo karshen yakin da Hamas.

Dermer ya ce barin masu kishin Islama da ke samun goyon bayan Iran zai gayyato kai hare-hare ba tare da izini ba a kan Isra'ila daga ko'ina cikin yankin: "Kuma shi ya sa kudurin fitar da Hamas ya yi karfi sosai, koda kuwa hakan zai iya haifar da baraka da Amurka."

Blinken-Egypt
Blinken-Egypt

Yayin da take goyan bayan manufofin yakin Isra'ila, gwamnatin Biden ta girgiza matuka sakamakon yawaitar kashe fararen hular Falasdinawa.

Harin ya kashe kusan Falasdinawa 32,000, in ji ma'aikatar lafiya ta Gaza, ba tare da samar da adadin fararen hula da mayaka ba. Hamas ta kashe mutane 1,200 a Isra'ila a ranar 7 ga Oktoba tare da sace 253, bisa ga kididdigar Isra'ila.

Isra'ila ta ce ta kashe ta kama da kuma tarwatsa isassun mayakan Hamas don tarwatsa bataliyoyinta 18 daga cikin 24, yayin da aka kashe sojojin Isra'ila 252 a farmakin.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG