Ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov sun tattauna batutuwan da suka shafi moriyar juna da kuma zaman lafiyar yankin a birnin Moscow ranar Laraba.
Babban jami’in ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya yi wani sabon gargadi yau Alhamis cewa sama da mutane 780,000 suka rasa matsugunansu a Mozambique, mafi yawansu saboda tada kayar baya na tsawon shekaru bakwai da kungiyar jihadi ta yi wanda ya jefa arewacin kasar cikin rudani.
Nikki Haley Ta kawo karshen yunkurin da take yi na samun tikitin yiwa jam’iyyarta ta Republican takarar shugabancin Amurka.
Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon Shugaban Kasar Donald Trump na daf da samun tikitin yiwa jam’iyyunsu na Democrats da Republican takara.
Kamala Harris ta ce ya kamata kungiyar Hamas ta amince da yarjejeniyar tsagaita wutan, ta kuma yi kira ga gwamnatin Firai Minista Benjamin Netanyahu da ta dauki matakin kara kai agaji a Gaza.
Akalla Falasdinawa 104 ne aka kashe a birnin Gaza ranar Alhamis yayin da sojojin Isra’ila suka bude wuta kan mutanen da ke kokarin samun abinci daga manyan motocin jin kai.
Firai Ministan Isra'ila ya fada a ranar Lahadi cewa, yuwuwar tsagaita wuta a yakin da kasarsa ke yi da mayakan Hamas zai jinkirta kai hari ta kasa ne kawai a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda ya zama mafaka ga fiye da rabin al'ummar yankin da ke fuskantar rikici.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umurci babban bankin Najeriya CBN ya biya wani Bajamushe, Martin Gegenheimer Naira miliyan 63.7 da dala 10,000 bisa kama shi da tsare shi da hukumar kula da shige da fice ta Najeriya NIS ta yi ba bisa ka'ida ba.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi a ranar Litinin cewa, rashin abinci mai gina jiki, da kuma yaduwar cututtuka na iya haifar da kazamin mutuwar yara a Gaza.
Duk Litinin ta uku a watan Fabrairu, Amurkawa na gudanar da bukin ranar Shugaban Kasa.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.