Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Karbe Ikon Yankuna 5 A Gabashin Donetsk Na Kasar Ukraine


Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin

A ranar Juma’a kafar yada labaran Rasha ta ruwaito ma’aikatar tsaron kasar na cewa, dakarun ta sun karbe iko kan wurare 5 a yaknkin gabashin Donetsk na Ukraine.

A ranar Juma’a kafar yada labaran Rasha ta ruwaito ma’aikatar tsaron kasar na cewa, dakarun ta sun karbe iko kan wurare 5 a yaknkin gabashin Donetsk na Ukraine, da ya hada da kauyen Novomoskovsk.

Rahoton da ya fito daga kafar sadarwa ta Rasha, Ria Novosti tace, dakarun Rasha sunyi galaba akan wata tankar yaki, da bangarorin soji 4 da wata rundunar yaki guda da manyan kusoshin yakin Ukraine 3, na sojin ruwa 2, na dakarun tsaron iyaka 3 dana dakarun tsaron kasa 2.

Rundunar ta kuma yi nasarar dakile hare hare har 68, duk da dai ba’a tantance hakan ba. Rahoton na rasha yazo ne a dai dai lokacin da ministan tsaron Ukraine, Rustem Umerov ke birnin Stockholm a jiya Juma’a domin halartar taro, da takwaran shi na Sweden, Pal Johnson. Johnson ya sanar da cewa, Swedin, wadda daya ce daga cikin sabbin manbobin kungiyar kawancen tsaro ta NATO, tayi alkawarin bayar da tallafin dala bilyan 2.2 ga Ukraine a shekarar 2025 da 2026, ya kara da cewa, akwai zurrfaffan hadin kai tsakanin kasashen biyu.

A yayin wani taron hadin guiwa na manema labarai, ministocin tsaron biyu sun tattauna irin yankan kaunar da Rasha keyi a halin yanzu, da ya hada da harin da Rashan ta kaddamar da makami mai linzami mai cin matsakaicin zango, kan birnin Dnipro.

Johnson yace, Sweden ta kira kaddamar da harin da wani yunkuri na jefa mu su tsoro da sauran kasashe daga taimakama Ukraine, da yace Rashan ta fadi ba nauyi. Johnson ya shaidawa Umerov cewa, tallafin Sweden ga Ukraine yiwa kai ne, saboda tsaron Ukraine, tsaron kasar Sweden ne.

A cikin wani jawabin kafar Talabijin da aka yada a fadin kasar a ranar Alhamis, shugaban Rasha Vladimir Putin ya tabbatar da kaddamar da harin makamin mai linzami dake cin dogon zango, wanda da farko Ukraine tayi zargin, hari ne na makamin ballistic, a matsayin martani ga lamincewar da Amurka da Birtaniya su kayiwa Kyiv na tayi amfani da makamai masu linzami dake cin dogon zango a kan Rasha.

A cikin jawabin, Putin yayi gargadin cewa, zai iya yin amfani da sabon makami mai cin nisan kilomita 800, akan wadannan kasashen. Wasu masu sharhi, irin su Keir Giles na Chatham House da ke Birtaniya, ya kira kaddamar da harin makami mai linzamin da lafazin Putin a matsayin salon tsoratarwa. Yace abu na karshe da Putin zai so yi shine, kai hari kan wata memba ta NATO.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG