Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Isra’ila Da Hezbollah Ta Fara Aiki A Lebanon


Rikicin gabas ta tsakiya
Rikicin gabas ta tsakiya

Da sanyin safiyar Larabar nan ne dai yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta fara aiki, lamarin da ya kawo dakatar da yakin da shugabannin Amurka da na Faransa suka ce zai iya samar da wata hanyar da za a sake yin sulhu a zirin Gaza.

A yayin da tsagaita wutar ta fara aiki, anga jerin motoci sun nufi kudancin Lebanon, inda aka shafe watanni ana gwabza kazamin fada da kuma umarnin Isra'ila na tilastawa mutane barin gidajensu.

Sojojin Isra'ila sun gargadi mutane da su kaurace wa kauyukan da a baya suka ba da umarnin ficewa.

Amurka tare da Faransa sun taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikicin, wanda majalisar ministocin tsaron Isra'ila ta amince da shi da yammacin jiya Talata.

Shugaban Amurka Joe Biden ya kira tsagaita wutan “Mataki mai mahimmanci… don kawo karshen tashin hankali” a Gabas ta Tsakiya. Ya ce Iran da 'yan ta'addanta, Hezbollah a Lebanon da kuma mayakan Hamas a Gaza, “sun yabawa aya zakinta” a cikin sama da shekara guda suna fafatawa da sojojin Isra'ila.

Ya ce yarjejeniyar Isra'ila da Hizbullah “an tsara ta ne domin ta zama ta dindindin ta dakatar da yaki.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG