Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za A Yafe Wa Sojoji Sabbin Dauka Bashi A Rasha


Shugaban kasar Vladimir Putin
Shugaban kasar Vladimir Putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wata doka da ke bai wa sabbin sojojin da aka dauka domin yaki a Ukraine yafe musu bashi.

Matakin, wanda aka kafe a shafin yanar gizon gwamnati ranar Asabar, ya jaddada bukatar sojoji ga Rasha a yakin da aka shafe kusan shekaru 3 ana gwabzawa, duk da cewa ta harba wani sabon makami mai linzami mai cin dogon zango a makon da ya gabata.

A cewar kafar yada labaran Interfax, sabuwar dokar ta ba da dama a yafe wa mutanen da suka aikin soja a matsayin 'yan kwantaragi tsawon shekara basussukan kudi da ake bin da suka kai rubles miliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka 96,000. Dokar ta shafi basussukan da kotu ta bada umarnin a karba kuma an fara aiki akansu kafin ranar 1 ga watan Disamba na 2024. Hakazalika dokar ta yafe wa mata ko mazan (ma'aurata) wadanda suka shiga aikin sojan bashin da ake binsu.

Kasar Rasha ta kara kaimi wajen daukar aikin soji ta hanyar ba da tallafin kudi ga masu son yin yaki a Ukraine.

Wannan matakin ya ba sojojin kasar damar karfafa mukaman soja a wurin da ake rikici yayin da ya kaucewa sake fidda umurnin gwamnati na girke sojojin kasar na musamman da daukar karin sojoji aiki. Wani kwarya-kwaryan irin wannan matakin da aka dauka a watan Satumba ya sa dubban maza 'yan Rasha guduwa daga kasar don kaucewa shiga aikin soja.

Yakin da aka dade ana yi kuma ya shafi jami'ai da kayan aikin Rasha sosai. Shi ya sa a watan Disamba Putin ya ne a dauki Karin sojoji 180,000 aiki.

Ma'aikatar Tsaro ta Ukraine a ranar Lahadi ta nuna wa kamfanin dillacin labarai na Associated Press tarkacen sabon makami mai linzami mai cin dogon zango, wanda ya afkawa wata masana'anta a tsakiyar birnin Dnipro na kasar Ukraine ranar Alhamis.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG