Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araghchi ya sabunta kiran da ya yi na a tsagaita wuta a Gaza da kuma Lebanon a ranar Asabar, yayin da yake tattaunawa da kawayen kasarsa na Siriya.
Ya shaida wa manema labarai cewa, “Batun da ya fi muhimmanci a yau shine tsagaita wuta, musamman a Lebanon da kuma Gaza.”
“Akwai shirye-shirye game da wannan, akwai tuntubar juna da muke fatan za’a yi nasara.”
Ziyarar Araghchi a Damascus, babban birnin kasar Siriya, wadda itace ta farko tun bayan da aka nada shi a watan Agustan da ya gabata, na zuwa ne kusan shekara guda bayan mayakan kungiyar Hamas ta Falasdinawa da ke samun goyon bayan Iran suka kai hari kan Isira’ila, lamarin da ya haifar da yaki a Gaza.
kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon, wacce abokiyar Iran ce ta kuma shiga cikin rikicin kuma a ranar 23 ga watan Satumba Isira’ila ta tsananta kai hari kan mayakan kunigyar.
“Manufar tafiya ta zuwa Damascus ita ce ci gaba da tuntubar juna game da abubuwan da ke faruwa a yankin,” in ji Araghchi.
Taron nasa a babban birnin kasar Siriya ya biyo bayan ziyarar da ya kai a birnin Beruit a ranar Juma’a, inda ya bayyana goyon bayan sa ga yarjejeniya a kasar Lebanon, wanda kungiyar Hezbollah ta amince da ita “a lokacin guda tare da tsagaita wuta a Gaza.”
Araghchi ya tafi Damascus ta jirgin sama bayan da Lebanon ta ce wani harin da Isira’ila ta kai a ranar Juma’a ya katse babbar hanyar kasa da kasa da ta hada kasashen biyu.
Isira’ila ta ce ta kai harin ne da nufin hana kawarar makamai zuwa ga kungiyar Hezbollah daga makwabciyarta Siriya.
Iran ta kasance babbar ta hannun damar shugaban Siriya Bashar al-Assad a tsawon yakin basasar da ya barke a shekarar ta 2011 bayan murkushe zanga-zangar adawa da gwamnati.
AFP
Dandalin Mu Tattauna