Rundunar ‘yansandan babban birnin Najeriya Abuja ta tabbatar da aukuwar tashin bam a wata makarantar Islamiyya mai suna Tsangayar Sani Usthman a kauyen Kuchibiyu da ke karamar hukumar Bwari.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Josephine Adeh ta ce an sami harin bam din ne da misalin karfe goma sha daya na safen ranar litinin.
“Bayan samun kiran gaggawa daga sarkin Kuchibiyu mun tura tawagar ‘yansanda harda wadanda suka kware kan cire bam, wanda suka killace gurin tare da kwashe wadanda suka ji raunuka zuwa asibiti.”
Sannan ta kara da cewa “ya zuwa yanzu bincike ya nuna ana zargi wasu mutane uku daga Katsina da suka ziyarci mai makarantar Malam Adamu Ashimu da cewa su suka kawo abunda da ya fashe kuma ya haddasa mutuwar mutum biyu daga cikin su. Yayin da dayan da kuma wata mace mai sayar da kaya suka sami raunuka.”
Tuni dai ‘yan sanda sun tafi da mai makarantar Malam Adamu Ashimu domin amsa tambayoyi.
~Alhassan Bala~
Dandalin Mu Tattauna